Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Yadda zaku Gane fake alert


 Yanda Zaku Gane Fake Alert.


Naga wasu suna koyarda yanda akeyin fake alert hakan yasa nace bari na koyamaku yanda zaku gane fake alert.


Kayi saving kuma kuyi sharing.


kullum scammers suna zuwa da sababbin hanyoyin yaud*rar al’umma daga ciki hada fake alert, wanda mutane suna yawan fadawa a wannan tarkon, hakan yanasa suna tafka asara musamman yan kasuwa abun akwai tausayi


Wannan itace hanyarda zaku gane fake alert.


Note!


Ba kowane yakasance mutumin banza ba kafin ka zargi wani akan fake alert Ka tabbatar Ka karanta wannan rubutun cikin natsuwa kuma ka kiyaye abubuwanda na zayyano.


1- A duk lokacinda wani wanda baka saniba ya turamaka kudi, idan har baka yarda dashi ba, kamar yanda na fadamaku a baya cewa ba kowane azzalum! ba.


koda ya turamaka payment receipt kuma kaga alert, abunda zakayi shine kayi transfer din kudin zuwa ga wani bank account dinka idan fake alert ne zakaga ance maka insuffient account balance, ma’ana kudin ba zasu fitaba saidai ka gansu a numbers.


Ku kiyaye akwai banbanci tsakanin matsalar network da kuma fake transfer.


Idan babu network kudin ba zasu shiga cikin account dinka ba, transfer zata iya zama pending koda kuwa sunyi debiting din abokin kasuwancinka, ita kuma fake transfer zasu nuna maka cewa kudin sun shiga amma kuma ba zasu fita ba saboda haka a kiyaye wannan.


2- Idan kana hada hadar kudi dayawa yanada kyau ka ware wani account daban wanda zaka rinka karbar kudi daga strangers ma’ana mutanenda baka saniba, wannan shine zai baka damar tantancewa cikin sauki a lokacinda bukatar hakan ta tashi.

Post a Comment

0 Comments