Ga wasu hanyoyi da zaka iya gane fake alert:
1. Duba Saƙon Banki Kai Tsaye, Kar Ka Dogara da SMS kawai:
Fake alert yawanci ana aikowa ne da karya SMS daga waya ko ta app.
Ka shiga banking app ɗinka ko ka kira customer care domin tabbatar da cewa kudin sun shiga asusun ka na gaske.
2. Tabbatar da Balance (Ragowar Kudi) a Account:
Idan mutum ya ce ya tura kudi, ka duba balance naka.
Idan balance bai ƙaru ba, to akwai matsala.
3. Email na Banki:
Yawanci idan an samu kudi na gaske, banki na aika maka da email.
Fake alert ba ya iya zuwa da email ɗin banki na gaskiya.
4. Lokacin Shigowar Kudi:
A SMS na gaske, zaka ga cikakken bayani kamar:
Sunan mai tura kudin,
Adadin kudi,
Ranar da lokaci.
Fake alert yawanci suna da kuskure a cikin waɗannan bayanai, ko font ɗin sakon ya bambanta.
5. Idan Ana Bukatar Zama Mai Tsaro: POS ko Shop:
Amfani da na'urar da ke haɗi da banki kai tsaye (POS original ko App na banki).
Kada ka yarda da screenshot kawai. Screenshot na iya zama hoto na karya.
6. Tabbatar da Sender:
Idan ba a saba samun kudade daga wannan mutumin ba, ka tabbatar sosai kafin kayi releasing kaya ko sabis.
A takaice:
Kada ka dogara da SMS ko screenshot! Ka duba account ɗinka kai tsaye kafin ka yarda cewa an biya ka.


0 Comments