Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kashi 99 na ɗaliban da su ka maimaita UTME sakamakon matsalar na'ura sun samu maki ƙasa da 200 - JAMB


 Kashi 99 na ɗaliban da su ka maimaita UTME sakamakon matsalar na'ura sun samu maki ƙasa da 200 - JAMB


Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta sanar da cewa kashi 99 cikin 100 na ɗalibai 336,845 da suka sake zana jarrabawar UTME ta bana a Legas da jihohin Kudu maso Gabas biyar sun samu kasa da maki 200.


Jaridar The Guardian ta rawaito cewa hakan na nufin ɗalibai 333,477 da suka samu kasa da maki 200 cikin 400.


A wata sanarwa da kakakin JAMB,  Dr. Fabian Benjamin, ya fitar a yau Lahadi, hukumar ta bayyana cewa, ‘yan kadan ne kawai suka samu maki 217 daga waɗanda subka maimaita jarrabawar.


Da ya ke fitar da sakamakon jarabawar ta UTME da aka sake yi a ranar Lahadin da ta gabata bayan tangarɗar na'ura da ta kawo cikas a jihohi shida na Tarayyar, Dokta Benjamin ya ce daliban tun farko basu samu maki mai yawa ba, haka zalika da aka maimaita ma ba su samu ba.

Post a Comment

0 Comments