Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Menene GitHub?




GitHub wata shahararriyar dandamali ce da ake amfani da ita don adana, tsara, da raba lambar shirye-shirye (code). Yana ba masu haɓaka damar aiki tare a kan software project guda, ko suna kusa da juna ko a wurare daban-daban a duniya.


📅 Wace Shekara Aka Fara Amfani da GitHub?


GitHub ya fara aiki a shekarar 2008, kuma tun daga lokacin ya zama ginshiƙi wajen ci gaban software da Open Source.


💡 Me ake amfani da GitHub?


 • Adana lambar shirye-shirye (code) cikin tsari

 • Gudanar da versions na code (version control)

 • Haɗin gwiwa tsakanin masu shirya manhajoji

 • Gina CV ta fannin coding

 • Aikace-aikace da bincike na AI, Cybersecurity, Web Developme


Idan kai ɗalibi ne a fannin Computer Science, Software Engineering, ko wani abu da ya shafi fasaha (tech), ka fara amfani da GitHub tun yanzu!

 • Yana taimakawa ka koyi yadda ake aikin professional software development

 • Zai nuna kwarewarka ga masu daukar aiki (employers)

 • Zaka iya yin projects naka ko shiga cikin Open Source Projects



Post a Comment

0 Comments