Idan Kanada yaro wanda ya fara tasowa misalin Shekara goma zuwa sama, yanada kyau Ka siya mashi computer idan kanada hali, computer tanada matukar amfani ga yaro musamman wadanda sukeda zimmar neman ilimi.
Ga Kadan daga cikin fa'idojin computer ga yara.
A bangaren "Cognitive benefits"
1- tana taimaka ma yara domin sanin yanda zasu warware matsaloli masu sarkakiya (Problem solving skills)
2- Tana taimakawa yara akan abunda ya shafi neman ilimi tahanyar amfani da softwares dakuma online resources.
3- Computer tana taimakawa yara wajen logical thinking tahanyar amfani da logical concept irinsu algorithm, da sequence, yaronda ya iya operating computer zaka sameshi yanada Kaifin basira.
A bangaren "Social benefits"
1- Idan mukayi duba a wannan lokacinda muke ciki na digital age zamuga cewa ilimin computer yanada matukar tasiri ga yara akan abunda ya shafi future nasu musamman yanda ilimin technology ya zama jari kuma yazama hanyar dogaro dakai.
2- ilimin computer yana taimakawa yara wajen "Confidence" yaro wanda yakeda ilimin computer zaka sameshi yanada confidence.
A bangaren "Creativity"
1- Computer tana taimakawa yara domin zama creative tahanyar amfani da softwares wadanda suka shafi design, rubutu DSS
2- Zai taimaka ma yara domin Koyon abunda ya shafi Digital skills kamar video editing, graphics design, dasauran digital skills wanda zasu taimaka masu domin dogaro dakansu.

0 Comments