Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne dan takara ɗaya tilo


 Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne dan takara ɗaya tilo na shugabancin kasa a jam’iyyar, bisa amincewar Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC).


A cewar Ganduje:


> “A matsayina na shugaban jam’iyya kuma a madadin Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC), wanda shine kadai dandalin da aka amince da shi bisa doka wajen tura dan takara a kowanne zabe, ina tabbatar da goyon bayan da aka samu kuma ina bayyana Shugaba Tinubu a matsayin dan takara ɗaya tilo na shugaban kasa a Jam'iyyar APC.”


Wannan furuci na zuwa ne bayan taron Koli na jam'iyyar da ya gudana a Fadar Shugaban kasa.


Ganduje ya kara da cewa, wannan mataki yana nuna karfin hadin kai da dandalin jam’iyya ke da shi wajen mara wa Tinubu baya, tare da nuna cewa babu wani dan takara na gaba da zai kara da shi a karkashin APC.

Post a Comment

0 Comments