Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Gwamnatin Najeriya za ta sayar da gidajen Emefiele 753 ga masu ƙaramin ƙarfi

                                               Birnin Tarayyar Najeriya Abuja
 

Da yake zantawa da jaridar PUNCH a ranar Asabar, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar gidaje, Badamasi Haiba, ya ce gwamnati, ƙarƙashin wani shirin Shugaba Bola Tinubu, za ta tabbatar da cewa talakawan Najeriya sun amfana.

Hukumar dake Yaki da cin hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ce ta bankado makeken rukunin da ya kunshi gidaje har 753 a wata unguwa dake Abuja.

A cewar hukumar ta EFCC, wannan shine kwace mafi girma da aka yi na ƙaddarori a lokaci guda tun kafuwar hukumar a shekarar 2003, duba da cewa filin na da faɗin murabba'in mita 150,000 kuma ta haɗa da gine-gine bine da ake kira duplexes da sauran gidaje.

Mai shari’a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja ya bayar da umurnin kwace rukunin gidajen a ranar 2 ga watan Disamban shekarar 2024.

Post a Comment

0 Comments