Muhimmancin koyon Tech Skills
1- High demand: Tech Skills yakasance daya daga cikin iliminda yake tafiya da zamani hakan ne yasa kamfanoni, da manyan kungiyoyi kamar NGOs, suke neman wadanda sukeda kwarewa akan abunda yashafi ilimin tech.
2- Career opportunities: wadanda sukeda ilimi akan abunda yashafi tech skills sunada damarmaki dayawa a bangaren samun aiki daga kamfanoni daban daban.
3- Flexibility and remote work: Tech skills yanada saukin aiki wanda zai iya baka damar yin aiki daga inda kake ma'ana zaka iya yin aiki a gida tahanyar amfani da yanar gizo (internet)
4- Creativity and innovation: Tech skills zai taimaka maka wajen sanin yanda zaka warware manyan matsaloli, tareda sanin yanda zaka iya kirkirar sababbin abubuwa wanda suka hada da sababbin fasahohi, damarmakin kasuwanci, ko hanyoyin samun kudi, domin dogaro dakanka.
5- Continuous learning: duba dacewa a kullum ana samun sababbin fasahohi na zamani hakan zai baka damar cigaba da koyon sababbin abubuwa, domin kara zurfafa iliminka tareda inganta tunaninka.
6- Higher earning potential: Duba da muhimmancin tech skills ga kamfanoni hakan zai baka damar samun biya mai inganci idan kana aiki a kamfani ko kana aiki ne a matsayin freelancer.
7- Global opportunities: Zai baka damar samun damarmakin aiki a ko Ina a fadin duniya.
8- Empowerment and independence: Zai baka damar dogaro dakanka koda yakasance cewa baka samu aiki ba, tahanyar Zama freelancer wanda zai baka damar aiki ga mutane daban daban domin dogaro dakanka.
Kuyi register da Jaez Digital Academy domin Koyon tech skills a cikin sauki.

0 Comments