Mafi yawan lokaci idan muka ziyarci shafuka a yanar gizo muna cin karo da wata tambaya akan cewa "accept cookies" wasu website din bazasu bamu damar wucewa face sai idan munyi accepting, minene cookies minene fa'idarshi?
Let's break it down
Cookies file ne wanda website yake storing a wayar mutane a lokacinda suka ziyarci website din a ranar farko usually ya kunshi rubutu, hakan yana ba website damar sanin dabi'un visitors wanda ya shafi yare, dasauran abunda sukafi mayarda hankali akanshi a lokacinda suka ziyarci yanar gizo.
YANDA COOKIES YAKE AIKI
1- a lokacin farko daka ziyarci website yana ajiye cookies a wayarka, idan kayi accepting.
2- kamfani yana amfani da cookies a matsayin identity gareka aduk lokacinda ka kara ziyartar website dinsu.
3- kamfani yana amfani da cookies domin sanin halayyar masu ziyartar website din, kamar yare, dabi'un wanda suka shafi kalar content dinda kafi bukata, tareda login details dinka, so baka bukatar ka kara login a lokacinda ka kara ziyartar website din.
4- kamfani yana amfani da cookies domin sanin kalar tallace tallacenda za'a rinka nuna maka, wanda sukayi daidai da ra'ayinka
Kamar misalin Temu duk lokacinda kayi engaging akan wasu kalar product, kayi attempt ko searching akansu , a kowane lokaci kalar wannan product din zasu rinka nuna maka dukda cewa akwai products daban daban.


0 Comments